Smart Contracts: Amfaninsa da yadda NEAR Protocol ke gudanar da shi.

Near Hausa Community
4 min readApr 23, 2024

Tun asalin ta, fasahar blockchain ta kasance jigo a wajen kawo canji a bangarori na rayuwar mu daban-daban, sannan da shigowar Decentralized finance (DeFi) a matsayin bangare mai karfi a cikin blockchain an samu bullowar wata fasaha wacce ita ce take tafiyar da DeFi din da muke amfani da a yau da kullum. Wannan fasahar itace smart contracts. Smart contracts code ne mai aiki da kansa wanda ake rubuta shi a kan computer. Sannan NEAR Protocol, a matsayin sa na babban blockchain mai tafiyar da kansa a kan wannan tsarin na smart contracts yana amfani da smart contracts ta hanyoyi daban-daban. Ku biyo ni sannu a hankali domin sannin cikakken bayani a kan Smart Contract, amfanin su da kuma yadda NEAR Protocol ke amfani dashi.

Menene Smart Contracts

Domin fahimtar smart contracts (yarjejeniya), akwai bukatar mu fahimci yadda yarjejeniya ke aiki. A yarjejeniya tsakanin mutane, kamar wadda ake yi tsakanin mai karbar hayar gida da kuma mai bada wa. Ana bukatar dillali wanda shi zai zama mutum na uku wanda zai kawo mai doka ko kuma lawya wanda zai tabbatar da cewa gaba daya mutanen biyu sun cika dokokin da suke cikin wannan yarjejeniya. Kuma da zaran an rattaba hannu, to ya zama dole garesu su bi abinda wannan yarjejeniyar ta kunsa. Smart Contracts, wata yarjejeniya ce wacce ake rubuta ta da code a compputer kuma bata bukatar mutum na uku ko dillali domin ganin an cika wadannan dokoki saboda ita ta kan tabbatar da hakan ya faru ta hanyar programming, sannan duk wanda ya ki cika dokokin wannan yarjejeniya a cikin mutanen da suka rattaba hannun, to zata aiwatar da abinda ya dace gwargwadon dokokin da aka gudanar da ita a kai.

Smart Contracts on NEAR Protocol

NEAR Protocol suna bayar da framework mai karfi inda developers zasu kirkiri decentralized applications dApps masu amfani da smart contracts kuma masu aiki a wajaje da yawa. Ga misalin manyan abubuwan da Smart Contracts a NEAR suke badawa.

1. Scalability: Sharding architecture na NEAR Protocol yana bawa smart contracts damar faruwa a tare, cikin hanzari kuma da tabbatar da cewa mutane da yawa zasu iya yin hada hada da yawa a lokaci a cikin sakan daya. Wannan damar, ta tabbatar da cewa manhajoji a kan NEAR zasu yi amfani komin yawan mutanen da suke kan su.

2. Rashin Tsada: Tsarin tattalin arzikin NEAR yana tabbatar da cewa za’a iya yin duk hada hadar da za’a yi cikin kwanciyar hankali ba tare da ana tunanin tsada ba. Developers zasu iya rubuta smart contracts dinsu sannan suyi amfani da blockchain din ba tare da sunyi tunanin tsadar gas fee ba. Hakan ya kawo sauki gare su da kuma sauran mutane masu amfani da manhajojin.

3. Tsaro: NEAR Protocol sun bada muhimmanci sosai ga tsaro, inda suka tabbatar da wani mechanism mai karfi domin bawa smart contracts tsaro da kuma magance matsalolin da zasu zo a gaba. Ta hanyar verification, auditing da kuma best practices na smart contract development, NEAR suna da niyyar kawo fage mai tsaro domin wallafa manhajoji masu yin aikin da aka kirkire su domin shi.

4. Usability: NEAR suna bada muhimmanci sosai ga jin dadinn developers wajen kirkirar manhajojin su domin ta yin hakan ne zasu samu damar kirkirar manhajojin cikin kwanciyar hankali. Shi yasa suka dage tukuru wajen kawo tools masu yawa, documentation da kuma libraries domin taimakawa wajen kirkirar smart contracts. Haka zalika, kasancewar NEAR sun kawo manya manyan sanannun frameworks da IDE (integrated development enviroment) ya kawo sauki wajen developing manhajojin.

5. Interoperability: NEAR Protocol an yi shi ne da niyyar samar da sauki wajen interoperability, hakan ya bawa smart contracts din da suke kan NEAR damar yin interaction da smart contract din da suke kan sauran blockchain cikin sauki

Amfanin Smart Contracts A NEAR

  • Decentralized Finance (DeFi): Smart contracts, sune kashin bayan da ke tafiyar da harkan decenralized finance kamar su lending and borrowing platforms, decentralized exchanges (DEXs), da sauransu.
  • Management na Supply Chain: Ta hanyar recording na transactions a ledger domin kasancewa kowa yana iya ganin su, a kan yi amfani da smart contracts wajen tracking na kaya daga inda a ka loda su zuwa inda za’a kai su a duk fadin duniya. Hakan yana rage zambo kuma yana tabbatar da transparency.
  • Buga wasanni (Gaming): Ana amfani da smart contracts wajen kirkirar decentralized gaming platforms, hakan yana bada dama ga masu buga wadannan wasannin wajen yin cinikayyar in game assets. Misali (NFT’s na Zomland)

Tabbas Smart contracts ginshiki ne na NEAR Protocol. Kuma a cikin niyyar NEAR na tabbatar da tsarin democradiyya a wajen kirkirar manhajojin da suke kan tsarin decentralization dApps da kuma ci gaban tattalin arziki. Bugu da kari, wajen mai da hankali wajen tsaro, scalability, usabiliyi da kuma interoperability, NEAR Protocol sun kawo wani platform ga developers domin kirkire-kirkiren su hankali kwance. Kamar yadda fasaahar blockchain take ci gaba a kullum, tabbas smart contracts a NEAR protocol suna da muhimmiyar rawar da zasu taka domin tabbatar da karbuwar wannan fasahar da mu ke so kuma muke amfani da ita a yau da kullum.

Ku ci gaba da biyo mu a shafen mu na telegram da kuma X domin samun bayanai a kan near protocol da kuma amsar tambayoyin ku a kan duk abunda ya shafi NearProtocol. Muna kawo shirye shirye daban daban masu ilmantar da mutane a kan blockchain musamman NEAR protocol. Bugu da ƙari akwai giveaway da muke yi da kuma “Zealy task” da muke yi duk wata. Shin kuna son ku san nawa ake bawa wanda ya fi kowa hazaƙa a zealy task ɗinmu ? ku biyo mu telegram.

Sai kun zo.

#NEARProtocol #NEAR #BOS

--

--